Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci Amurka da ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan Venezuela
2020-03-30 21:25:18        cri
Kasar Sin ta bukaci kasar Amurka, da ta martaba ka'idoji da muhimman dokokin MDD da suka shafi alakar kasa da kasa, ta kuma daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Venezuela.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Madam Hua Chunying ce ta bayyana haka yau, yayin taron manema labarai da ya gudana a nan birnin Beijing lokacin da take mayar da martani kan rahotanni da kafofin watsa labarai suka bayyana cewa, a ranar 26 ga watan Maris, ma'aikatar shari'ar Amurka ta tuhumi shugaba Nicolas Maduro na kasar Venezuela da mai taimaka masa kan laifin fataucin miyagun kwayoyi, har ma ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya ladan dala miliyan 15 ga duk wanda ya taimaka mata da bayanan da za su kai ga kama wa ko hukunta Maduro.

Madam Hua ta jaddada cewa, kasar Venezuela, kasa ce mai 'yanci da kuma cin gashin kanta, don haka har kullum kasar Sin tana adawa da duk wata kasar waje dake kokarin shiga harkokin cikin gidan kasar Venezuela ta ko wace hanya, kana tana adana da sanya mata takunkumin da ya sabawa doka.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China