Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na fatan Amurka za ta ba da karin taimako wajen tabbatar da hana yaduwar makaman nukiliya a duniya
2020-06-08 20:25:32        cri

Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Litinin a nan Beijing cewa, kasar Sin na fatan kasar Amurka za ta saurari kiran da kasashen duniya ke yi, ta kuma ba da karin taimako wajen tabbatar da kwance damarar makaman nukiliya da hana yaduwar su a duniya, da ma hana kawo illa ga zaman lafiyar duniya.

Rahotanni sun nuna cewa, wata tawagar kungiyar kula da yarjejeniyar hana gwaje-gwajen nukiliya daga dukkan fannoni ta ba da wata sanarwa a kwanan baya, inda ta nuna damuwa sosai kan wasu rahotannin dake cewa, Amurka na tattaunawa kan yiwuwar sake yin gwaje-gwajen makaman nukiliya. Tawagar ta jaddada cewa, idan Amurka ta yi hakan, hakika za a dawo da gwaje-gwajen nukiliya a duniya, kuma hakan na iya lalata tsarin yarjejeniyar. Don haka tawagar ta yi kira ga kasashen duniya da su sake nanata goyon bayansu kan yarjejeniyar, tare da daukar matakai don ganin yarjejeniyar ta fara aiki cikin hanzari. Kasar Rasha ta riga ta nuna goyon bayanta kan sanarwar. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China