Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashen Afirka ba za su yarda a haddasa rashin jituwa tsakaninsu da kasar Sin ba
2020-06-12 20:26:32        cri

Hua Chunyin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Jumma'a a nan Beijing cewa, shaidu sun sha nuna cewa, kasashen Afirka sun ki yarda a haddasa rashin jituwa a tsakaninsu da kasar Sin.

Rahotanni na cewa, a kwanan baya, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya ce, kasarsa ta lura da cewa, kasar Sin da kamfanoni masu zaman kansu na kasar sun bai wa kasashen Afirka taimako da bai taka kara ya karya ba. Sin za ta bai wa kasashen Afirka rancen kudi ta hanyar da ba ta dace ba a daidai wannan lokacin da ake fama da annobar COVID-19, hakan wani salo ne na jibgawa kasashen Afirka basussuka da yawa.

Dangane da kalaman Pompeo, madam Hua Chunying ta jaddada cewa, yanzu kasashen Afirka na fuskantar kalubale a fannoni daban daban. Kasar Sin na fatan sassa masu ruwa da tsaki za su mai da hankali kan taimakawa kasashen Afirka wajen yaki da annobar, za su kuma girmama jama'ar Afirka. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China