Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yi watsi da shirin Amurka na sa hannu kan kudurin dokar kare hakkin dan Adam ta Uygur ta shekarar 2020 don ya zama doka
2020-06-18 11:52:14        cri

Kasar Amurka ta sa hannu kan shirin dokar kare hakkin dan Adam ta Uygur ta shekarar 2020 don ya zama doka.

Yau Alhamis 18 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen ksar Sin ta ba da wata sanarwar, wadda a cikin ta aka bayyana cewa, wannan shirin doka ya bata sunan jihar Xinjiang ta kasar Sin, a fannin kare hakkin dan Adam, ya kuma sossoki manufofin kasar Sin, game da tafiyar da harkokin jihar Xinjiang, kana ya saba wa dokokin kasa da kasa, da kuma muhimman ka'idojin raya hulda a tsakanin kasa da kasa, ya kuma zama mataki na tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin. Don haka gwamantin Sin da jama'ar kasar, sun fusata da hakan, sun kuma bayyana kin yarda da wannan mataki na Amurka.

Sanarwar ta ce, batun Xinjiang, batu ne da ke shafar yaki da 'yan ta'adda da 'yan a-ware, ba wai batu ne na hakkin dan Adam, ko kabilu ko addini ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China