Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta aiwatar da martani ga tarnakin da ake yiwa 'yan jaridar kasar a Amurka
2020-03-18 09:52:52        cri

A shekarun baya bayan nan, gwamnatin Amurka na ci gaba da kakaba wasu tarnaki ga kafofin watsa labaran kasar Sin, da jami'an dake aiki da su a Amurkar, wanda hakan ke hana su gudanar da ayyukan su cikin sauki, tare da nuna musu kyama, da amfani da siyasa wajen cusguna musu.

Sakamakon hakan, ita ma Sin ta ayyana daukar matakan martani da suka hada da umartar kafofin watsa labarai na Muryar Amurka, da "The New York Times", da "The Wall Street Journal", da "The Washington Post Time" da su rubuto cikakkun bayanai game da ma'aikatan su, da harkokin kudaden gudanarwar su, da tsarin ayyukan su da kuma matsugunnan su a kasar Sin.

Kaza lika, kamar yadda Amurka ta nemi kafofin watsa labarin Sin da su rage yawan ma'aikatan su dake Amurkar, ita ma Sin ta umarci Amurkawa dake aiki da kamfofin watsa labaran "New York Times", da "The Wall Street Journal" da "The Washington Post" wadanda takardun aikin su za su kare kafin karshen shekarar nan ta 2020, da su sanar da sashen lura da bayanai na ma'aikatar harkokin wajen Sin cikin kwanaki 4 masu zuwa tun daga yau Laraba, kana su mika katunan shaidar aikin su ga sashen cikin kwanaki 10 masu zuwa.

Matakin na nufin ba za su samu damar ci gaba da aiki a matsayin 'yan jarida a daukacin kasar Sin ciki hadda yankunan musamman na Hong Kong, da Macao ba.

Mataki na uku shi ne, kamar yadda Amurka ta kakaba takunkumi ga 'yan jaridar Sin dake aiki a Amurka bisa batun ba da visa, da tantance ayyukan gudanarwa da ba da rahotanni, Sin za ta dauki makamancin wannan mataki kan 'yan jaridun Amurka dake Sin.

Mahukuntan Sin dai sun ce daukar wadannan matakai sun zama wajibi, kuma martani ne da ya zama wajibi Sin ta dauka, sakamakon yadda ake yiwa kafofin watsa labaru da 'yan jaridar kasar dake aiki a Amurka matsayin lamba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China