2020-06-11 20:36:49 cri |
Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Alhamis a nan Beijing cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta girmama hakikanin abubuwa, ta daina kallon duniya bisa ra'ayinta, ta dakatar da tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin da sunan addinai.
Madam Hua ta bayyana haka ne, yayin da take mayar da martani kan rahoton da Amurka ta gabatar a kwanan baya, inda ta soki manufofin kasar Sin ta fuskar addinai. Madam Hua ta kara da cewa, akwai damuwa matuka kan yadda al'ummomi marasa rinjaye suke bin addini a Amurka. A duk lokacin da Amurka ta fitar da irin wannan rahoto, ta kan bayyana rashin gaskiyarta da ma fuska biyu da take nunawa kan harkokin addini. (Tasallah Yuan)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China