Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai kimanin dubu 500
2020-07-08 13:38:12        cri
Cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afrika, ta fitar da alkaluma a jiya Talata dake nuna cewa, yawan mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a Afrika ya kai mutum 494,380, kana yawan mamata a nahiyar ya kai 11,652, inda kuma wasu 238,287 suka warke daga cutar.

Bisa alkaluman da aka fitar, cutar ta fi kamari ne a kasashen Afrika ta kudu, da Masar, da Najeriya da Ghana. Sauran sun hada da Aljeriya, da Moroco, da Kamaru da kuma Cote D'ivore. Inda a Afrika ta kudu kadai, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya kai fiye da mutum dubu 200, kana a Masar adadin ya kai fiye da dubu70, yayin da a Najeriya kuma ya kai dubu 20.

Fadar shugaban kasar Gambia ta ba da rahoto a jiya cewa, shugaban kasar Adama Barrow, ya yanke hukuncin tsawaita lokacin ko ta kwana a kasar da kwanaki 7, tun daga ranar 8 ga wata, inda ake ci gaba da daukar wasu matakai na hana cudanyar jama'a.

Ban da wannan kuma, gwamnatin Angola ta bayyana a jiya cewa, karuwar yawan mamata sakamakon cutar ya jawo damuwa matuka, sabili da haka, ta tsawaita lokacin bude makarantu, bayan da a baya aka tsaida ranar 13 ga wata domin sake bude su. Ministan kiwon lafiya na kasar ya ce, ana nazartar matakan da ake dauka don yakar cutar, kuma mai yiwuwa a dauki matakai na daban don dakile cutar. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China