Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwesi Quartey: Alakar Sin da Afirka na bunkasa a sassa daban daban
2020-05-27 10:09:07        cri

Mataimakin shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Kwesi Quartey, ya ce dadaddiyar alakar dake tsakanin Sin da nahiyar Afirka za ta ci gaba da bunkasa, kamar dai yadda ake ganin hakan, yayin da sassan biyu ke kara inganta hadin gwiwa mai kunshe da tarihi da burin ci gaba iri daya.

Kwesi Quartey ya ce yayin da cutar COVID-19 ke kara bazuwa a Afirka, gwamnatin Sin da kamfanonin ta, na ci gaba da nuna goyon baya da tallafi ga kasashen Afirka, a yakin da ake yi da wannan annoba, ta hanyar mika taimakon kayayyakin kiwon lafiya da nahiyar ke matukar bukata.

Jami'in ya jaddada cewa, gina helkwatar kungiyar AU, mataki ne dake nuni ga kyakkyawar alakar Sin da Afirka, ya kuma jinjinawa Sin, bisa taimakon ta ga Afirka a matakai daban daban, ciki hadda a wannan lokaci na yaduwar annoba.

Da yake tsokaci game da darasin da duniya ya dace ta koya daga wannan cuta, Kwesi ya ce akwai bukatar karfafa tsarin kiwon lafiyar al'umma, da kuma fadada goyon baya da hadin kai tsakanin kasashe, da yankuna, da nahiyoyi da dai sauran su, domin shawo kan irin wadannan kalubale tare.

Da yake gabatar da na sa ra'ayi, shugaban tawagar Sin a kungiyar AU Liu Yuxi, ya ce Sin ba ta taba mantawa da goyon bayan da Afirka ta nuna mata, a lokacin da take tsaka da yaki da wannan annoba ba, wanda hakan ya nuna dankon zumunta dake tsakanin sassan biyu.

Liu Yuxi, ya kara da cewa, baya ga tallafin kayayyakin kiwon lafiya, Sin na ci gaba da agazawa kasashen Afirka wajen gabatar da kwarewar da ta samu, a yaki da annobar, baya ga tura jami'an lafiya zuwa sassan nahiyar da dama, domin su tallafawa ayyukan yaki da cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China