Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: An keta hakkokin yara sama da 25,000 yayin da ake rikici a shekarar 2019
2020-06-16 12:52:41        cri

Rahoton shekara-shekara kan yara da rikice-rikice da Sakatare Janar na MDD ya fitar jiya, ya ce an keta hakkokin yara sama da 25,000 yayin da ake rikice-rikice a shekarar 2019.

Jimilar adadin ya yi daidai da wanda aka samu a shekarar 2018, wanda kuma ke nuna ana keta hakkokin yara 70 a ko wace rana. A cewar rahoton, wadanda ba 'yan kasa ba ne suka aikata sama da rabin laifin.

Ana ci gaba da samun karancin rahoton laifukan fyade da sauran nau'ikan cin zarafi ta hanyar lalata, inda aka tabbatar da samun laifuka 735 masu nasaba da su a shekarar 2019. Laifukan sun fi kamari a kasashen Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Somalia da Afrika ta Tsakiya da Sudan da Sudan ta Kudu.

MDD ta kuma tabbatar da cewa, an sace yara 1,683 a shekarar 2019, mafi yawansu a kasashen Somalia da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Nijeriya. An sace yaran ne don horar da su ko cin zarafi ta hanyar lalata ko kuma don neman kudin fansa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China