Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Darektan CDC ta Afrika : Taron koli na hadin kan Sin da Afrika wajen yakar COVID-19 na ba da taimako kara karfin hadin kansu a fannin kiwon lafiya
2020-06-19 13:20:31        cri

Darektan CDC ta Afrika John Nkengasong ya shaidawa manema labarai cewa, Afrika na fuskantar matsaloli da dama ta fuskar kiwon lafiya, kuma taron koli na hadin kan Sin da Afrika wajen yakar COVID-19 da aka yi a wannan karo ya zurfafa hadin kan Sin da Afrika a wannan fanni.

A cewarsa, ban da yaduwar cutar a halin yanzu a nahiyar, ana kuma fuskantar kalubalen cutar sida, da cutar tarin fuka, da zazzabin cizon sauro. Ya ce, taron da aka yi a wannan karo ya inganta hadin kan Sin da Afrika, ta fuskar yakar cutar COVID-19, har ma ya habaka zuwa fannin kiwon lafiya, da dai sauran bangarorin dake da nasaba da wannan fanni.

Dadin dadawa, John Nkengasong ya jinjinawa hadin kan Sin da Afrika, wanda a ganinsa, hadin kai ne da kuma taimako juna, bisa zumunci da mutunta juna mai haifar da moriyar juna.

Ban da wannan kuma, a cewarsa, tushen hadin kan bangarorin biyu, shi ne zumunci da mutunta juna, ya ce, ya kamata sauran kasashe su koyi darussa daga salon hadin kan Sin da Afrika. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China