Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutane 268,000 sun kamu da COVID-19 a Afrika kana 7,000 sun mutu
2020-06-19 15:41:37        cri

Nahiyar Afrika ta ba da rahoton mutane 268,391 sun kamu da cutar COVID-19, yayin mutane 7,217 annobar ta kashe, sannan adadin mutanen da suka warke daga cutar ya kai 123,139 a nahiyar, hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ne ta sanar da hakan a ranar Alhamis.

Kawo yanzu dukkan kasashen Afrika 54 an samu bullar cutar COVID-19, inda kasar Afrika ta Kudu ce ta fi yawan masu dauke da cutar, inda masu dauke da cutar sun kai 83,890 a kasar. Sai kuma kasashen Masar, Najeriya, Ghana, da Aljeriya suna daga cikin kasashen da cutar tafi kamari a nahiyar. Masar tana da kusan mutane 50,000 masu dauke da cutar, sai Najeriya mai mutane 18,000, yayin da Ghana da Aljeriya suna da mutane sama da 10,000 da aka tabbatar sun harbu da cutar, a bisa sabbin alkaluman da Afrika CDC ta fitar ranar Alhamis. (Ahamd Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China