Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta sake tura kayayyakin kandagarkin cuta zuwa Afrika ta Tsakiya
2020-06-13 16:05:14        cri

A ranar 11 ga wata bisa agogon jamhuriyar Afrika ta tsakiya, an gudanar da bikin mika kayayyakin kandagarkin cutar COVID-19, da kasar Sin ta baiwa kasar a matsayin tallafi jeri na 2, a filin saukar jiragen sama dake Bangui, fadar mulkin kasar. Inda shugaban kasar Afirka ta Tsakiya Faustin Touadera, da jakadan kasar Sin a kasar Chen Dong, gami da sauran manyan kusoshin sassa daban daban, suka halarci bikin.

A wajen bikin, shugaba Touadera ya shaidawa jakada Chen na kasar Sin cewa, gwamnatin kasar Sin da jama'arta, sun kai dauki ga jama'ar kasar Afirka ta Tsakiya, jim kadan bayan sun tsunduma cikin mawuyacin hali na fama da annoba, saboda haka yana matukar godiya ga kasar Sin.

A nasa bangaren, ministan lafiya na kasar Afirka ta Tsakiya, mista Pierre Somse, ya ce, kasarsa ba za ta samu ainihin alkaluma game da yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 ba, balle ma jinyarsu da kubutar da su, in ba dan na'urorin gwajin cuta da kasar Sin ta ba ta ba. Saboda haka, a cewarsa, samun goyon baya daga kasar Sin, shi ne tushen aikin yakar cutar COVID-19 a kasar Afirka ta Tsakiya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China