Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar 'yan kasuwar Afrika dake Guangzhou ta shiga babban taron baje kolin harkokin ciniki da ake yi ta yanar gizo
2020-06-19 13:17:52        cri

An kaddamar da babban taron baje kolin harkokin ciniki na birnin Guangzhou da ake yi ta yanar gizo karo na 127 a ran 15 ga wata a birnin Guangzhou. Jiya Alhamis kuma, kungiyar 'yan kasuwar Afrika ta lardin Guangdong da kuma sassanta dake birnin Guangzhou sun yi taro a Guangzhou, inda 'yan kasuwa na kasashen Afrika suka bayyana kwarin gwiwarsu kan babban taro da kuma hadin kan Sin da Afrika ta fuskar ciniki, tare kuma da hadin kansu wajen ingiza 'yan kasuwar Afrika da su shiga babban taron.

Kungiyar 'yan kasuwar Afrika ta lardin Guangdong ta nuna cewa, taron da aka yi a wannan karo na ba da damar ganewa idanu wasu kayayyaki a kafar Intanet, kanana da matsakaitan kamfanoni na Afrika za su iya yin oda da sayen kayayyaki ta Intanet, ta wannan hanya ba ma kawai za su iya ganewa idanunsu ingancin kayayyaki ba, har ma ziyarartar wasu kamfanoni.

Shugaban kungiyar 'yan kasuwar Kamaru Okuma ya bayyana cewa, wannan sabon salo na baiwa masu sayayya damar fahimtar ingancin kayayyakin kasar Sin a kan Intanet, kuma suna iya zaba cikin kamfanoni daban-daban masu dimbin yawa. A sa'i daya kuma, yawan kayayyakin da za a saya zai karu sosai, 'yan kasuwa kimanin 100 za su shiga wannan taro, yawacinsu sun shiga taro da kuma yin oda da sayan kayayyaki a kan Intanet. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China