2020-07-03 09:55:43 cri |
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira ga kwamitin sulhu na MDD, da ya dauki matakan da suka dace na ganin an amsa kiran da babban sakataren MDD ya yi na tsagaita wuta a fadin duniya, a gabar da daukacin duniya ke fama da matsalar COVID-19.
Zhang Jun ya ce, yayin da kwamitin sulhun ya amince da kudirin dake goyon bayan matakin babban sakataren na MDD, ya kamata kwamitin sulhun ya yi kokarin ganin wannan buri ya tabbata.
Jami'in wanda ya bayyana haka, yayin mahawarar manyan jami'ai kan tasirin da COVID-19 ta haifar ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa, ya ce ya kamata al'umomin kasa da kasa su yi amfani da wannan dama wajen karfafawa sassan dake fada da juna gwiwar amsa wannan kira su kuma harzarta tsagaita bude wuta, su hada hannu wajen yaki da wannan annoba, da ceton rayuka da sasantawa ta hanyar matakai na siyasa da diflomasiya.
Haka kuma Zhang, ya bukaci kwamitin sulhun, da ya samar da tallafin jin kai da daukar matakan da suka kamata don tabbatar da tsaro da kare rayukan ma'aikatan wanzar da zaman lafiya.
Ya kara da cewa, ya kamata kwamitin sulhun ya bukaci kasashen da abin ya shafa, da su hanzarta dage takunkumin da aka iya shafar karfin kasashe na yaki da COVID-19. Bugu da kari, ya dace kwamitin sulhun ya bullo da hanyoyin kawar da matakai na tilastawa, don rage kuncin da al'ummomi a kasashen da abin ya shafa ke fuskanta.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China