Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya yi kira da a mutunta 'yancin kasashe kan matakan kare hakkin dan Adam
2020-02-14 11:14:17        cri
Jakadan kasar Sin dake MDD Wu Haitao ya yi kira da a mutunta 'yancin kasashen da abin ya shafa kan matakan da suke dauka game da abubuwan da suka shafi kare hakkin dan Adam.

Kare hakkin dan Adam yana daya daga cikin muhimman bangarorin dake tabbatar da gina tubalin zaman lafiya, kuma ya kamata a daga matsayin manufofin gina zaman lafiya da kuma samun dawwamamman zaman lafiyar. Tilas ne duk wata tattaunawa da za'a gudanar ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rikici da abubuwan dake biyo bayan bankewar rikicin, in ji Wu Haitao, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD.

Game da wannan batu, yana da matukar muhimmanci a mutunta 'yancin kasashen da abin ya shafa karkashin ka'idojin MDD da kuma dokokin da kasa da kasa suka amince da su, Wu ya bayyana hakan ne ga kwamitin sulhun MDD, a lokacin taron kwamitin game da batun.

Ya ce akwai bukatar a mutunta matsayin kasashen da abin ya shafa a kokarinsu na tabbatar da adalci ta hanyar daukar matakai bi da bi karkashin tsarin da ya dace da yanayin da kasashen suke ciki. Bai kamata a tursasa wata kasa don shigar mata da wani salo daga ketare ba, bai kamata a yi shisshigi cikin harkokin gudanarwar wata kasa ba ko kuma yin katsalandan cikin al'amurran wata kasa ba.

Wu ya ce, ta hanyar girmama ikon da kasashe suke da shi ne kadai za'a samu cikakken adalci, da samun amincewar kasashen da abin ya shafa, kuma hakan shi ne hanyar tabbatar samun zaman lafiya da ci gaba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China