Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta yabawa goyon bayan da take samu daga MDD wajen yaki da cutar Corona
2020-02-08 20:01:44        cri

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya bayyana godiyarsa ga irin goyon bayan da MDD take ba kasar Sin wajen yaki da cutar Corona.

Zhang Jun ya bayyana haka ne a jiya, yayin da yake ganawa da Mourad Wahba, mukaddashin shugaban shirin raya kasashe na MDD UNDP.

Yayin ganawar, Mourad Wahba, ya gabatar da wasika daga shugaban shirin UNDP Achim Steiner zuwa ga shugabannin kasar Sin, game da matakan kariya da dakile yaduwar cutar Corona, inda ya bayyana yakinin da Shirin UNDP ke da shi kan kasar Sin, da kuma goyon bayansa ga al'ummar Sinawa da kuma kudurinsa na bada duk wani taimako da ake bukata.

A nasa bangaren, Zhang Jun, ya bayyana kokarin da kasar Sin ke yi na yaki da cutar, inda ya ce an dauki matakai masu tsanani na dakile cutar, kuma ana samun sakamako mai gamsarwa. Ya kara da cewa, kasar Sin na da tabbacin za ta iya yakar cutar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China