Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD tana bukatar goyon bayan Sin don cimma burin raya kasa da kasa, in ji Ban Ki-moon
2019-12-23 14:00:58        cri
Kwanan baya, tsohon babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana cewa, bunkasuwar kasar Sin, da nauyin da kasar Sin ta dauka cikin harkokin kasa da kasa, da kuma goyon bayan kasar Sin kan raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, sun baiwa MDD babban taimako wajen cimma burinta na raya kasa da kasa.

Sau da dama cikin shekaru 10 da suka gabata, Ban Ki-moon ya sha ziyartar kasar Sin, ya kuma ganewa idanunsa bunkasuwar kasar cikin wadannan shekaru. Kuma abun da Mr. Ban yake mai da hankali shi ne, kasar Sin ta zama abun koyi ga sauran kasashe dake son neman dauwamammen ci gaba.

Cikin harkokin kasa da kasa, kasar Sin ta kan jaddada muhimmanci na kiyaye dangantakar dake tsakanin kasa da kasa domin neman ci gaba tare. A halin yanzu kuma, akwai wasu mutane dake fama da karancin abinci, kuma ba su sami kiyayewa kan ikonsu yadda ya kamata ba, don haka ake bukatar ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Kana hakan yana da muhimmanci wajen kiyaye tsarin kasa da kasa, da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, da kuma yin kira da a raya hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa.

A nan gaba kuma, Ban Ki-moon ya ce, yana fatan cikin dogon lokaci mai zuwa, kasar Sin za ta iya ba da jagoranci ga kasa da kasa kan harkokin siyasa, da tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, da al'adu da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China