Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta bukaci kasashe mambobin MDD su sauke nauyin dake wuyan su
2020-05-15 15:49:14        cri

Mukaddashin mataimakin wakilin dindindin na Sin a MDD Yao Shaojun, ya yi kira ga kasashe mambobin MDD, da su cika alkawuran tallafin kudi da suka dauka ga duniya. Yao ya shaidawa kwamiti na 5 na babban zaman MDD cewa, hakan zai yi matukar tasiri, musamman game da yaki da ake yi da cutar COVID-19

Jami'in ya kara da cewa, duk da cewa Sin na fuskantar matsin lamba ta fuskar tattalin arziki da harkokin kudi, sakamakon barkewar cutar COVID-19, duk da haka, a matsayin ta na kasa ta biyu mafi samar da kudaden kasafin kudin MDD na gudanarwa, da na ayyukan wanzar da zaman lafiya, ta yi kokarin ba da cikakken taimako da ya dace ta bayar, matakin da ya yi nuni ga hakikanin goyon bayan ta ga MDD.

Yao Shaojun ya ce Sin ta yanke kudurin ba da karin taimako na dalar Amurka miliyan 30 ga hukumar lafiya ta duniya WHO, ba ya ga tallafin dala miliyan 20 da tuni ta bayar ga hukumar.

Daga nan sai ya sake jaddada bukatar Sin, ta neman kasashe mambobin MDDr, musamman masu wadata, su gaggauta cika dukkanin alkawuran su yadda ya kamata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China