Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin Sin ya bayyana damuwa game da shirin mamayar Isra'ila kan matsugunan Falasdinawa
2020-05-21 11:19:43        cri

Wakilin kasar Sin ya ce kasarsa ta nuna damuwa matuka game da wasu rahotanni dake nuna cewa Isra'ila tana shirin fadada mamayar da take yi kan matsugunan Falastinawa.

Warware takaddamar dake tsakanin kasashen biyu ita ce kadai hanyar da za ta kawo karshen halin da al'ummar Falastinawa suke fuskanta. Kasar Sin ta bukaci dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su guji daukar matakin ra'ayin bangare guda kana su kaucewa haifar da tashin hankali da rikici, a cewar Zhang Jun, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD.

Zhang, ya fadawa taron kwamitin sulhun MDD cewa, kasar Sin tana kan matsayinta cewa babu wata kasa da za ta goyi bayan irin wannan ra'ayin na bangare guda. Ya kamata kwamitin sulhun MDD ya sauke nauyin dake bisa wuyansa sannan ya dauki matakan kariya daga wannan mummunan yunkuri, kana kwamitin ya maido da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Falastinawa da Isra'ila bisa yarjejeniyar MDD, da yarjejeniyar rikicin filaye, da yarjejeniyar zaman lafiya ta kasashen Larabawa.

Wakilin na Sin ya jaddada cewa, matsalar Falastinawa ita ce tushen rikicin yankin gabas ta tsakiya. Tabbatar da 'yantacciyar kasa hakki ne na al'ummar Falastinawa, kuma ba batu ne da za'a yi ta cece-kuce kansa ba.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China