Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ba da gudummawa matuka ga aikin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, in ji MDD
2019-12-12 14:00:03        cri
Daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga wata, an yi taron dandalin tattaunawa game da hakkin dan Adam na kasashe masu tasowa na shekarar 2019 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A yayin taron, mamban kwamitin nazarin hakkin dan Adam na MDD, kana shugaban kwamitin hakkin dan Adam na kasar Mauritius Dheerujlall Baramlall SEETULSINGH ya bayyana cewa, kasar Sin ta ba da babbar gudummawa ga raya aikin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, ta kuma ba da taimako mai ma'ana ga kasashe maso tasowa.

Haka kuma, ya ce, babban ci gaba da kasar Sin ta samu cikin shekaru da dama da suka gabata abun burgewa ne kwarai da gaske. Ya ce kasar Sin tana mai da hankali kan aikin kawar da talauci, wanda ya dace da burin MDD cikin jadawalin neman dauwamammen ci gaba ya zuwa shekarar 2030. Ban da haka kuma, kasar Sin tana taimaka wa kasashe masu tasowa wajen gina asibitoci, da inganta fasahohin ayyukan gona, da kuma taimaka musu wajen kyautata yanayin hakkin dan Adam, ciki har da wasu kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin ta ci gaba da karfafa mu'amalar dake tsakaninta da kasashe masu tasowa, lamarin da zai ba da taimako ga sauran kasashe masu tasowa, wajen samun ci gaba kamar yadda kasar Sin ta samu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China