Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya bayyana manar aladun bikin Duanwu
2020-06-25 14:26:51        cri
"Al'adu yana nuna halin wata kasa", bayan babban taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin karo na 18, kwamitin tsakiyar JKS ya fara mai da hankali matuka kan ci gaban al'adun gargajiyar kasar Sin. Sau da dama, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada muhimmancin yaduwar al'adun kasar Sin, da kuma karfafa amincewar al'ummomi kan al'adun kasa.

Yau ranar 25 ga watan Yuni, ranar ce da Sinawa suke murnar bikin Duanwu. Kuma, a yau, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi mana bayani kan wannan bikin gargajiyar kasar Sin.

Dinka kananan jakunkuna masu kamshi, cin Zongzi, da kuma tseren kwale-kwale da sauransu, dukkansu sun zama al'adun gargajiya na kasar Sin domin taya murnar bikin Duanwu. A kan sa magungunan gargajiya masu kamshi a cikin kananan jakunkuna, domin kau da kwari da rigakafin cututtuka. A garin Mazhuang na birnin Xuzhou na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, Wang Xiuying mai shekaru 80 da haihuwa ta yi gadon fasahar gargajiya ta dinka kananan jakunkuna masu kamshi, har dinka kananan jakunkuna masu kamshi da hannaye ya zama sana'a ta musamman a wannan wuri.

A watan 12 na shekarar 2017, Xi Jinping ya taba kai ziyarar aiki ofishin dinka kananan jakunkuna masu kamshi na garin Mazhuang, da ya duba kananan jakunkuna masu kamshi da mutanen garin suka dinka, inda ya yaba matuka, har ya sayi wata da Wang Xiuying ta dinka.

A lokacin ziyararsa a garin, Xi Jinping ya sa kaimi ga Wang Xiuying cewa, ya kamata a ci gaba da yada wannan fasahar tarihi a fannin al'adu da aka gada daga kaka da kakanni, wato dinka kananan jakunkuna masu kamshi dake cike da magungunan gargajiya. A kuma yada wannan fasaha ga kowa da kowa domin raya al'adun kasar Sin baki daya.

A halin yanzu, kananan jakunkuna masu kamshi da garin Mazhuang ya samar sun samu karbuwa a wurare daban daban na kasar Sin, har ma, an sayar da su zuwa kasashen waje da dama, kamar kasar Burtaniya da kasar Japan da sauransu. lamarin da ya sa, aka yada wannan al'adu zuwa kasashen duniya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China