Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Sin da kasashen Turai sun sake jaddada niyyarsu ta daddale yarjejeniyar zuba jari a bana
2020-06-22 19:58:34        cri

Yau Litinin firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya jagoranci ganawar shugabannin Sin da EU karo na 22 tare da shugaban kungiyar kasashen Turai Charles Michel da shugaban hukumar gudanarwar EU Ursula von der Leyen.

Game da yarjejeniyar zuba jari ta Sin da EU, shugabannin sassan biyu sun bayyana cewa, sun ga ci gaban da aka samu, kuma za su ci gaba da yin kokari domin daddale ta a bana, kana sassan biyu sun yarda cewa za su tattauna kan abubuwan dake shafar yin takara bisa adalci, kuma suna sa ran za su cimma matsaya guda ba tare da bata lokaci ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China