Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya gana da sabbin shugabannin EU
2020-06-23 10:54:53        cri

A jiya Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da shugaban majalisar Turai Charles Michel, da shugabar kwamitin EU Ursula von der Leyen ta kafar bidiyo.

Shugabannin sun yi shawarwari a karo na 22 da shugaban Sin a wannan rana. A yayin ganawar da aka yi bayan shawarwarin, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin na neman zaman lafiya, ba wai mallake duniya ba, kuma Sin na kasancewa dama ga dukkanin duniya maimakon kalubale. A hannu guda ita abokiya ce ba kasar dake hamayya ba.

Ya ce ya kamata bangarorin Sin da Turai, su kara fahimtar juna, da nuna amincewa ga juna, don karfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu.

A nasu bangaren, Charles Michel da Ursula von der Leyen, sun bayyana cewa, bangaren Turai na son nuna sahihanci wajen gudanar da tattaunawa bisa manyan tsare-tsare da Sin, don kare ra'ayin bai daya, da kuma karfafa hadin kai da Sin, a fannonin nazarin allurar rigakafin cutar COVID-19, da sake komawa bakin aiki, kana da habaka fannonin cinikayya a tsakanin bangarorin biyu, da neman samun ci gaba a fannonin kiyaye muhalli, da tattalin arziki irin na fasahar zamani da dai sauransu, da gaggauta cimma yarjejeniyar zuba jari a tsakanin Turai da Sin, da kuma kokarta kawar da tasiri sakamakon yaduwar annoba, da inganta farfado da tattalin arzikin duniya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China