Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Don me kasar Sin ta tura jami'an kiwon lafiya zuwa kasashen duniya domin dakile COVID-19
2020-04-07 21:04:05        cri

A lokacin da kasar Sin take yakar cutar COVID-19 a tsakanin watan Janairu da na Maris, kasashen duniya masu dimbin yawa, kamar kasar Najeriya, da Italy sun goyi bayan kasar Sin, har ma sun samar da dimbin kayayyakin jinya ga kasar Sin.

A ran 2 ga watan Faburairu, shugaban kasar Nijeriya Mahammed Buhari ya tura wa shugaban kasar Sin Xi Jinping wani sako, inda ya jinjina, da kuma nuna goyon baya ga gwamnati da al'ummar Sinawa, wajen dakile cutar. Sakon shugaba Buhari ya burge Sinawa sosai. Bisa al'adar Sinawa, su kan mayar da martani ga wadanda suka taba taimaka musu.

Yanzu, yanayin fama da cutar da kasar Sin ke ciki ya samu sauki sosai, amma yanayin dakile cutar a galibin sauran kasashen duniya, ciki har da kasashen Amurka da Italiya da Spaniya da Faransa da Jamus da Afirka ta kudu da Nijeriya ya tsananta. Ya zuwa karshen Maris da ya gabata, bisa gayyatar da aka yi mata, kasar Sin ta tura wasu tawagogin jami'an kiwon lafiya 7, dake kunshe da daruruwan masu aikin jinya zuwa kasashe 6, kamar su Iran da Italiya, da Spaniya da Pakistan da Laos da Birtaniya.

A ganin Sinawa, kasar Nijeriya aminiya ce ta kasar Sin. Sabo da haka, bisa gayyatar da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi mata, hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta yanke shawarar tura wata tawagar kiwon lafiya mai kunshe da masanan kiwon lafiya 18 zuwa kasar Nijeriya.

A ganina, wannan albishiri ne ga kasar Nijeriya. Ko da yake, a ganin wasu mutanen Nijeriya, kawo yanzu yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar ba shi da yawa. Kuma jami'an kiwon lafiya na kasar Nijeriya suna kokari, da kuma cimma nasara sosai wajen shawo kan cutar. Amma kamar yadda Hausawa su kan ce, gidaje biyu maganin gobara. Ko da yake kasar Nijeriya tana kokarin dakile cutar, amma tana kuma fuskantar hadari sosai, sakamakon karuwar mutane masu harbu da cutar a yankunan dake makwabtaka da ita.

Bugu da kari, ba ta da isassun kayayyakin kiwon lafiya da ake bukata wajen dakile cutar. Wadannan ma'aikata masu aikin jinya na kasar Sin da ake da shirin tura su zuwa kasar, sun kware sosai wajen dakile cutar. Idan sun samu izinin zuwa kasar Nijeriya, za su iya ba da shawara idan takwarorinsu na Nijeriya suna bukatar aikin jinya ga wadanda suka kamu da cutar, kamar yadda suke yi a kasashen Italiya da Spaniya da Iran da sauran kasashen duniya.

Alal misali, a lokacin da masanan kasar Sin suke kasar Italiya, su da takwarorinsu na Italiya, su kan tattauna kan matakan dakile cutar, da yanayin da wadanda suka kamu da cutar suke ciki, da matakan ceton marasa lafiya masu tsanani sosai da ya kamata a dauka ta kafar hoton bidiyo. Idan ba a gayyace su ba, ba sa shiga kowane asibiti, balle dakin kwana na marasa lafiya, ko dakin tiyata ko dakin ICU. Sakamakon kokarin da suka yi, sun samu yabo daga wajen al'ummar Italiya.

An labarta cewa, masanan kasar Sin sun je kasashen waje, sun kuma taimakawa takwarorinsu wajen dakile cutar COVID-19, ba domin neman kudi ba. A ganin Sinawa, yanzu mutanen duk duniya na zama ne tamkar a wani kauye guda, Idan wani ya gamu da bala'i daga indallahi, ko shakka ba bu, sauran al'ummun duniya ba su da damar gudu daga bala'in. Sabo da haka, ya kamata kowa ya bayar da gudummawarsa, wajen bunkasa wata kyakkyawar makoma ga daukacin bil Adama, maimakon cin moriya shi kadai, ta yadda za a iya tabbatar da ganin kowa ya samu alheri a nan gaba.

Muna fatan kasashen Sin da Nijeriya za su iya kara yin hadin gwiwa, kuma za su samu nasara ba a fannonin aikin gona, da kasuwanci kawai ba, wato ya kamata su karfafa zumunci, da hadin gwiwa a fannin kiwon lafiya, musamman yakin da ake yi da annobar COVID-19. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China