Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A shirye kasar Sin take ta ci gaba da taimakawa Mexico wajen yaki da COVID-19
2020-04-11 15:49:15        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce a shirye kasarsa take, ta ci gaba da taimakawa Mexico iya karfinta, wajen yaki da cutar COVID-19, ciki har da taimakawa kasar sayen kayayyakin da take tsananin bukata na yaki da annobar a kasar Sin.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne jiya, yayin da yake tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Mexico, Andres Manuel Lopez Obrador.

Bisa la'akari da yadda cutar ke ci gaba da bazuwa a Mexico da sauran kasashen da suke Latin Amurka da Caribbean, a madadin gwamnati da al'ummar kasar Sin, shugaba Xi ya jajanta tare da bayyana goyon baya ga gwamnati da al'ummar Mexico. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China