Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Paul Romer: Ya kamata Amurka ta koyi fasahohin birnin Wuhan wajen yaki da cutar COVID-19
2020-06-18 13:12:11        cri

A halin yanzu, kasar Amurka tana fuskantar da babbar matsalar yaduwar cutar numfashi ta COVID-19. Dangane da wannan lamari, Paul Romer, wanda ya taba lashe lambar yabo ta Nobel a fannin ilmin tattalin arziki a shekarar 2018, ya bayyana cewa, ya kamata kasar Amurka ta koyi fasahohin birnin Wuhan wajen yaki da annobar.

Ya ce, matakin da kasar Sin ta dauka, na yin gwajin cutar numfashi ta COVID-19 a duk fadin birnin Wuhan, ya ba da taimako matuka ga wannan birni, wajen dakile yaduwar annobar, don haka ya kamata, mu yi irin wannan gwaji a duk fadin kasar Amurka.

Ya kara da cewa, kafin samun allurar rigakafi, ya kamata kasar Amurka ta kara yin gwajin COVID-19. Kuma bisa hasashen da ya yi, gwajin cutar COVID-19, zai ba da damar cimma sakamako mai kyau, kasancewar mun ga yadda birnin Wuhan na kasar Sin, ya cimma nasara mai kyau, bisa gwajin da aka yi a duk fadin birnin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China