Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin watsa labaran Amurka sun sanar da bullar cutar numfashi da ba a san abin da ke haddasa ta ba da wuri a shekarar da ta gabata
2020-05-07 12:28:07        cri

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga kasashen duniya, da su yi kokarin gano wadanda suka kamu da COVID-19, bayan da bincike da dama suka nuna cewa, akwai mutane da tun farko suka kamu da wannan annoba a kasashe da dama. Bayanai na nuna cewa, an yi ta nuna damuwa game da barkewar cutar numfashi da ba a san abin da ke haddasa ta ba a watan Yulin shekararar 2019 a jihar Virgina dake Amurka.

Ita ma kafar watsa labarai ta ABC, ta bayar da rahoto a watan Yulin shekarar 2019, game da barkewar wata mummunan cutar numfashi mai kisa da ba a san abin da ke haddasa ta ba, har ma ta harbi mutane 54 a unguwar ma'aikatan da suka yi ritaya a jihar Virginia. Unguwar dake da nisan tafiyar sa'a guda a mota daga dakin binciken sinadarai, wanda aka rufe haka kwatsam a shekarar da ta gabata aka kuma sake bude ta nan da nan a wannan shekara.

A watan Agustan shekarar 2019, kuma, cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Amurka(CDC) ta bayar da umarnin rufe cibiyar nazarin cututtuta masu yaduwa ta sojojin kasar(USAMRIID) dake Detrik na wucin gadi.

A cewar jaridar NewYork Times ta Amurka, gwamnati ta dakatar da binciken da ake gudanarwa a cibiyar ce, saboda bullar wasu sinadarai masu guba da aka gano, wadda ke da matukar barazana ga lafiyar jama'a, da dabbobi da tsirrai ko albarkatun dabbobi da tsirrai.

A ranar 10 ga watan Maris kuma, an wallafa wani koke a shafin gabatar da koke na fadar White House ta Amurka, inda aka bukaci gwamnatin Amurka, da ta bayyana hakikanin daliliin rufe dakin binciken da ta yi a watan Agusta, sannan ta yi Karin haske, kan ko akwai kwayar cuta da ta sulale daga dakin binciken ko a'a.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China