Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta ba da karin shawarar amfani da marufin baki da hanci don yaki da COVID-19
2020-06-06 17:16:39        cri

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta sabunta ka'idojinta na amfani da marufin baki da hanci wajen dakile yaduwar COVID-19, inda ta shawarci jama'a masu shekaru 60 zuwa sama, da wadanda ke da wasu matsaloli, su rika sanya marufin a inda ba za su iya kaucewa taron jama'a ba.

Sabuwar ka'idar na shawartar sanya marufin baki da hanci irin na likitoci ga dukkan ma'akatan jinya a inda ake fuskantar bazuwar cutar, ba wadanda ke mu'amala da masu cutar kadai ba.

Wato misali, idan likita na duba mara lafiya a sassan da babu masu cutar, duk da haka, kamata ya yi ya sanya marufin baki da hanci.

Sabuwar ka'idar, ta kuma shawarci jama'a kan amfani da marufin a inda ake samun yaduwar cutar.

A cewar sakatare janar na WHO Tedros Adhnom Ghebreyesus, bisa la'akari da shaidun da ake samu, WHO na shawartar gwamnatoci su karfafawa al'ummu gwiwar sanya marufin baki da hanci a inda ake samun yaduwar cutar da wuraren taron jama'a.

Sai dai, hukumar ta yi gargadin cewa, sanya marufin ba ya nufin maye gurbin matakin nisantar jama'a, ko tsaftar hannu ko sauran wasu matakan kandagarki, ta na mai cewa, marufin na da muhimmanci a matsayin wani bangare na muhimman dabarun yaki da COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China