Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO ta ce za a dakatar da amfani da maganin malaria wajen gwajin magance cutar COVID-19
2020-06-18 10:23:58        cri

A jiya Laraba ne kwararru a hukumar lafiya ta duniya WHO, suka bayyana cewa, za a dakatar da amfani da kwayar magani ta hydroxychloroquine, a aikin gwajin maganin cutar numfashi ta COVID-19, duba da cewa, kawo yanzu kwayar maganin ba ta samar da wata fa'ida wajen kawar da cutar ba.

A cewar masanan, bincike ya nuna cewa, kwayar hydroxychloroquine wanda a baya ake amfani da ita wajen magance zazzabin cizon sauro, ba ta yi wani tasiri a fannin yakar COVID-19 ba.

Ana Maria Henao Restrepo, jami'ar lafiya a sashen alluran rigakafi da gwaje gwajen halittu a hukumar WHO, ita ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a birnin Geneva.

Jami'ar ta kara da cewa, bayan gudanar da jerin gwaje gwaje da kwayar maganin, an gano cewa, hydroxychloroquine, bai samar da wata fa'ida a fannin rage rasuwar masu dauke da cutar COVID-19 da ke kwance a asibitoci ba. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China