Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Dage dokar rufe birane sannu a hankali ce mataki mafi dacewa ga raya tattalin arziki da shawo kan COVID-19
2020-05-12 10:27:31        cri
Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce yayin da kasashen duniya ke dage dokar zaman gida ga al'umma, da ma sauran matakai na kulle domin yakar cutar COVID-19, matakan dage irin wadannan dokoki sannu a hankali, za su taimaka wajen farfado da tattalin arziki, da ma karfafa matakan shawo kan cutar.

Kaza lika hakan a cewar sa, zai ba da damar sanya ido sosai, ga yanayin yaduwar cutar domin gano bakin zaren dakile ta, idan har ta sake nuna alamun sabuwar yaduwa.

Da yake tsokaci yayin taron 'yan jaridu ta kafar bidiyo daga birnin Geneva, Mr. Ghebreyesus ya ce dokoki masu tsauri na kulle da kasashe daban daban suka dauka, sun taimaka kwarai wajen rage saurin yaduwar cutar, da kuma kare rayukan al'umma.

To sai dai kuma, jami'in ya ce sassauta matakan kulle yana da sarkaki da kuma wahalar aiwatarwa, tuni kuma aka fara ganin tasirin hakan a sassa daban daban cikin karshen makon da ya gabata. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China