Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin kasar Sin ya yi Karin haske kan sadaukarwa da hadin gwiwar yaki da COVID-19
2020-05-07 12:18:15        cri
Zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD dake Geneva Chen Xu, ya zayyana irin sadaukarwa da hadin gwiwar da kasashen duniya ke bayarwa kan yaki da cutar COVID-19.

Chen wanda ya bayyana haka yayin da yake jawabi a taron da aka kira ta kafar bidiyo, ya ce bai kamata kasashen duniya su bari zarge-zarge da wasu ke yi babu gaira babu dalili ya mayar da hannu agogo baya, a yakin da ake yi da wannan annoba ba. Haka kuma bai kamata a siyasantar da nuna kyama su rarraba kawuwa da yin fito na fito ba.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, a kullum kasar Sin na shiga a dama da ita a hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da COVID-19 ba tare da wata rufa-rufa ba, yadda ya kamata.

A cewarsa, kasar Sin ta taimakawa kimanin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 140, ta kuma shirya taruka ta kafar bidiyo da ma'aikata da masanan lafiya na kasashe sama da 150.

Haka kuma kasar Sin, ta bude cibiyar dabarun kandagarki da hana yaduwar COVID-19 da dukkan kasashe za su iya amfana. Yana mai cewa, a halin yanzu, dukkan kasashen duniya, suna aiwatar da matakan dakile annobar bisa yanayin da kasashensu ke ciki.

Wakilin na kasar Sin, ya ce, yana da muhimmanci a fahimci tare da martaba kokarin da kasashe daban-daban ke yi, da yin musaya da koyi da dabarun juna, ta yadda za a ga bayan wannan annoba baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China