2020-05-13 12:22:19 cri |
Cikin sharhin, an ce, a baya, kasashen duniya sun taba yin hadin gwiwa wajen yaki da cutar Ebola, da cutar Zika da kuma cutar kanjamau da dai sauransu, ana kuma ci gaba da kyautata aikin nazarin allurar rigakafi kan wadannan cututtuka, kuma kwararru da fasahohin da kasar Amurka ta samar, sun taka muhimmiyar rawa kan wannan aiki. Amma gwamnatin kasar Amurka ta ki yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya wajen yaki da cutar numfashi ta COVID-19.
Kaza lika Amurka ba ta halarci taron tattara kudade don yaki da cutar COVID-19, da sauran tarukan kasa da kasa masu nasaba da wannan aiki ba, tana kuma tattaunawa kan daukar matakai iri na kanta, lamarin da ya nuna cewa, kasar Amurka tana son bin hanyar "Amurka da farko". lallai abubuwan da kasar Amurka ta yi, za su gurgunta hadin gwiwar kasa da kasa kan wannan aiki, da kuma tayar da hankalin jama'ar kasa da kasa, lamarin da zai kasance wani babban kalubale ga duk duniya. (Maryam)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China