Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin ministan harkokin wajen Sin ya yi bayani kan sakamakon taron kolin Sin da Afirka na hadin gwiwar yaki da COVID-19
2020-06-18 13:11:17        cri
Jiya da dare, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron kolin Sin da Afirka na musamman kan hadin gwiwar yaki da COVID-19, ya kuma ba da jawabi mai taken "Yin hadin gwiwar yaki da COVID-19, cimma nasara cikin hadin gwiwa".

Bayan taron, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Chen Xiaodong, ya yi bayani kan sakamakon da aka cimma a wannan taro.

Ya ce, mahalarta taron sun yi musayar ra'ayoyi kan goyon bayan kasashen Afirka game da yaki da cutar, da kuma karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, da ma sauran kasashen duniya wajen yaki da cutar, inda suka cimma matsaya kan manyan batutuwan da abin ya shafa. An gabatar da sanarwar hadin gwiwa ta wannan taro, wadda ta bayyana matsayin shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka kan wasu manyan batutuwa.

Chen Xiaodong ya kara da cewa, an gudanar da wannan taro a lokacin da ya dace, taron zai yi muhimmin tasiri ga kasa da kasa. Da farko, zai inganta hadin gwiwar Sin da Afirka ta fuskar yaki da cutar COVID-19, sa'annan, ya nuna zamunci mai karfi dake tsakanin Sin da Afirka. A karshe dai, zai karfafa aniyar kasa da kasa don cimma nasarar yaki da annobar cikin sauri. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China