Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan tsaron kasar Sin ya gana da wakilan dandalin tsaro da zaman lafiya na Sin da Afirka
2019-07-18 09:33:40        cri
A jiya ne mamba a majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan tsaron kasar Wei Fenghe, ya gana da wakilan kasashen Afirka dake halartar taron dandalin zaman lafiya da tsaro na farko tsakanin Sin da Afirka da ake gudanarwa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Wei ya ce, hadin gwiwar tsaro da zaman lafiya muhimmin jigo ne a hadin gwiwar bangarorin biyu, don haka ya kamata Sin da Afirka su samu sabon ci gaba a hadin gwiwar dake tsakaninsu a wadannan sassa, su kuma ba da gudummawa ga ci gaban hadin gwiwar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare ta yadda za a inganta makomar al'ummomin kasashen biyu nan gaba.

A nasu jawaban, wakilan kasashen Afirka sun bayyana kudurinsu na yin aiki tare da kasar Sin, ta yadda za su zurfafa alaka a fannonin yiwa jiragen ruwan nahiyar rakiya, da yaki da ta'addanci, horas da jami'ai da atisayen hadin gwiwa da horo, ta yadda sassa biyu za su tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Afirka da ma duniya baki daya.

Wei ya kuma gana da ministocin tsaro daga kasashen Afirka 7 da suke halartar taron, gabanin ganawar sassan biyu. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China