Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wang Yi: Sin da Afirka suna da zumunci mai karfi
2020-04-14 16:29:39        cri
Jiya Litinin, wakilin majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da shugaban kwamitin kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat ta wayar tarho.

Dangane da wasu matsalolin da 'yan uwa na kasashen Afirka dake kasar Sin suka bayyana, kan yadda gwamnatocin sassan kasar Sin suke aiwatar da ayyukan kandagarki, da dakile yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, Wang Yi ya jaddada cewa, kasar Sin tana dukufa wajen kiyaye lafiya, da tsaron al'ummomin kasar Sin, da na kasashen ketare, ba ta taba nuna bambanci ga mutanen ketare dake kasar Sin ba, kuma ba ta daukar dukkanin matakan da za su nuna fuska biyu ba.

Ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka, suna da zumunci na gargajiya, wanda yake da karfi kwarai da gaske, kuma ba wani abun da zai bata zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka, balle ma mugun matakan da wasu kasashen suka dauka, domin bata dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka.

A halin yanzu, ana bukatar karfafa fahimtar juna, da goyon bayan juna, da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, domin cimma nasarar yaki da annobar cikin hadin gwiwa.

A nasa bangare kuma, Moussa Faki Mahamat ya ce, ba wani abu da zai bata zumuncin dake tsakanin kasashen Afirka da kasar Sin. Ya ce mun san kasar Sin tana dukufa wajen hana sake barkewar cutar numfashi ta COVID-19, kuma ana da imanin cewa, kasar Sin ba za ta dauki matakai masu nuna bambanci ba.

Ya kara da cewa, yana godiya matuka game da taimakon gaggawa da kasar Sin ta samarwa kasashen Afirka, domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19. Kana, wasu kasashen suna son yin amfani da wannan dama, wajen bata zumuncin dake tsakanin Afirka da Sin, kuma ko shakka babu ba za su cimma burin su ba. Har ila yau kasashen Afirka za su ci gaba da hadin gwiwa da kasar Sin. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China