Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Taron kolin hadin kan Sin da Afirka na yakar COVID-19 ya nuna ma'anar 'yan uwantaka komai wahala komai dadi
2020-06-16 19:43:23        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai shugabanci taron koli na musamman kan hadin gwiwar yaki da cutar COVID-19 tsakanin Sin da Afirka da za a bude gobe Laraba 17 ga wata a nan birnin Beijing tare da gabatar da jawabi

Game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Talata, cewa taron kolin da za a shirya ya kara nuna muhimmancin 'yan uwantaka komai wahala komai dadi.

Kakakin ya nuna cewa, ko da yaushe kasar Sin na mayar da hankali kan bunkasa kyakkyawar dangantakar hadin kai a tsakaninta da kasashen Afirka, da kokarin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga bangarorin biyu. Tun bayan bullar wannan annoba, kasar Sin da kasashen Afirka suna taimaka wa juna, da yakar cutar tare, abin da ya kara bunkasa dangantakar dake tsakaninsu.

Rahotanni na cewa, kasar Sin da kasar Afirka ta Kudu dake shugabancin karba-karba na kungiyar AU a wannan karo, da kuma kasar Senegal wadda ke shugabancin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, sun yi kira da a gudanar da taron ta kafar bidiyo, inda shugabannin kasashe membobin tawagar shugabancin taron koli na kungiyar AU, da kasashe dake shugabancin manyan kungiyoyin yankunan nahiyar Afirka da sauransu da kuma shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU za su halarci taron. Hakazalika kuma, babban sakataren MDD, da babban darektan hukumar kiwon lafiya ta duniya su ma za su halarci taron bisa gayyatar musamman da aka yi musu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China