Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin Sin da kamfanoninta sun samu yabo kan goyon baya ga Afrika a yaki da COVID-19
2020-05-14 11:03:06        cri
Yayin da ake cigaba da samun bazuwar annobar COVID-19 a nahiyar Afrika gami da karuwar bukatar da ake dashi na kai dauki domin dakile annobar, gwamnatin kasar Sin da kamfanonin kasar suna cigaba da samun yabo bisa ga irin goyon bayan da suke baiwa kasashen Afrika wajen yaki da annobar ta COVID-19.

A bisa ga alkaluma na baya bayan nan da cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Afrika (Africa CDC) ta fitar, adadin mutanen da cutar COVID-19 ta kashe a Afrika ya kai 2,403, yayin da yawan mutanen da suka kamu da cutar a nahiyar ya kai 69,578 ya zuwa yammacin ranar Laraba.

Kasar Sin, wacce a halin yanzu ita ma take yaki da annobar COVID-19 a cikin gida, tana kara taimakawa kasashen Afrika da kungiyoyin shiyyar domin tallafa musu wajen yaki da annobar a nahiyar.

A wani bangare na tallafin da kasar Sin ke baiwa Afrika wajen yaki da annobar COVID-19, gwamnatin Sin ta aike da tawagar kwararrun masana kiwon lafiya zuwa kasar Djibouti domin taimakawa jama'ar kasar yaki da cutar COVID-19, a ranar Litinin tawagar sun bar kasar bayan kammala muhimmin aikin da suka gudanar a kasar. A madadin gwamnatin kasar Djibouti, ministan harkokin wajen kasar Mahmoud Ali Youssouf, da ministan lafiyar kasar Mohamed Warsama Dirieh, sun halarci filin jiragen saman kasar domin bayar da lambar yabo ga tawagar bisa kokarin da tawagar suka yi ga kasar.

Domin taimakawa kasashen na Afrika wajen yaki da cutar COVID-19, gwamnatin Sin ta aike da tawagar masana kiwon lafiya zuwa kasashen Habasha, Burkina Faso, Djibouti, Cote d'Ivoire, Zimbabwe, Kongo DRC, da Algeria.

Haka zalika, akwai kimanin jami'an lafiyar kasar Sin kusan 1,000 da suka jima suna aiki a kasashen Afrika, kamar yadda hukumar lafiyar kasar Sin ta sanar da hakan.

A cikin watannin da suka gabata, gwamnatin kasar Sin da kamfanonin kasar sun bayar da tallafin kayayyakin kiwon lafiya ga kasashen Afrika, da suka hada da takunkumin rufe fuska, da kayayyakin dake baiwa jami'an lafiya kariya, da na'urar gwajin zafin jiki, da gilashin kare fuska, da safar hannu da takalman da jami'an lafiya ke amfani dasu, da sauran kayayyakin lafiya ga nahiyar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China