Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Lauyan Meng Wanzhou: Bankin HSBC ya nuna goyon baya ga Amurka wajen tsare Meng Wanzhou
2020-06-16 10:29:19        cri

Jiya Litinin, an sake sauraron karar Meng Wanzhou, a kotun kolin gundumar "British Columbia" dake kasar Canada, inda tawagar lauyoyin Meng Wanzhou ta gabatar da wani bayani ga kotun, inda ta bayyana cewa, bankin HSBC ya baiwa ma'aikatar shari'a ta kasar Amurka, shaidar da ta gabatar wa kotun Canada, domin maida Meng Wanzhou kasar Amurka. Amma wannan shaida tana cike da kuskure.

A halin yanzu, tawagar lauyoyin Meng Wanzhou ta bukaci a dakatar da shirin maida Meng Wanzhou kasar Amurka, bisa dalilan keta ka'ida, kuma babu isassun shaidu masu nasaba da hakan.

A wannan rana, kotun ba ta yanke hukunci kan karar ba, amma ta gabatar da lokacin sake sauraron karar Meng Wanzhou, wato a ranar 23 ga watan nan da muke ciki. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China