Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei zai ci gaba da taimakawa nahiyar Afrika yaki da COVID-19
2020-05-11 10:40:13        cri

Kamfanin Huawei ya yi alkawarin taimakawa kokarin nahiyar Afrika, wajen dakile yaduwar cutar COVID-19.

Cikin wani sharhi da aka wallafa a jaridar Standard, shugaban kamfanin a yankin kudancin Afrika Chen Lei, ya ce tsarin kamfanin na kiran bidiyo dake hada mutane da dama, ya taimaka wajen inganta tsarin sadarwa a asibitoci.

Ya kara da cewa, sun kuma fara amfani da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam wajen saukaka ayyukan duba mara lafiya a asibitoci. Yana mai cewa, za a iya nazarin hoton CT Scan cikin mintuna 2, abun da ya kara saurin aikin da kaso 80, lamarin ke da muhimmanci wajen ceton rayuka.

Ya ce kamfanin sadarwar na kasar Sin, zai ci gaba da amfani da karfin fasahar sadarwa wajen taimakawa kokarin nahiyar na yaki da COVID-19. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China