Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Matsin lambar Amurka ba zai hana Huawei ci gaba ba, in ji babban jami'in kamfanin
2019-06-17 18:54:51        cri
Babban jami'i kuma mamallakin babban kamfanin fasahar sadarwa na Huawei dake nan kasar Sin, Ren Zhengfei, ya ce matsin lambar Amurka, ba zai hana kamfanin na Huawei ci gaba ba.

Ren wanda ya bayyana hakan a Litinin din nan, ya ce bisa kiyasi, kudin shiga na kamfanin zai iya raguwa zuwa kusan dala biliyan 100 a bana, da shekarar dake tafe, amma kuma akwai hasashen farfadowar sa ya zuwa shekarar 2021.

Ren ya yi wannan tsokaci ne, yayin zantawar sa da masani a fannin hasashe dan kasar Amurka George Gilder, da Nicholas Negroponte, wanda ya kafa cibiyar binciken fasahar sadarwa ta jami'ar MIT, a birnin Shenzhen helkwatar kamfanin na Huawei. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China