2019-08-09 19:36:40 cri |
A yau ne katafaren kamfanin sadarwa na kasar Sin Huawei, ya gabatar da manhajarsa da ya kera da kansa a hukumance mai suna(OS) 'Harmanoy" wadda a baya ake kira HongmengOS.
Kamfanin ya gabatar da manhajar ce yayin taronsa na shekara-shekara da ya gudana a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.
Kafin gabatar da manhajar, shugaban kamfanin Richard Yu, ya bayyana dalilin kamfanin na gabatar da sabuwar manhajar, yana mai cewa, nan gaba mutane za su bukaci fasahohi na zamani wajen amfani da na'urori
Sabuwar manhajar ta OS tana da saukin amfani, da kuma matakan tsaro don biyan wadannan bukata, za kuma a yi amfani da ita a duk wani tsarin na'urorin intanet a nan gaba.
Kamfanin ya ce, za a fara amfani da manhajar ce a tsoffin na'urori, wayoyi na zamani, ababan hawa da lasifikoki na zamani.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China