Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Huawei ya sha alwashin bunkasa fasahohin sadarwa a Afirka
2019-10-31 09:38:38        cri

Shugaban kamfanin Huawei na kasar Sin Ren Zhengfei, ya ce kamfanin sa ya sha alwashin bunkasa ci gaban da fasahar sadarwa ke haifarwa a fannin raya tattalin arziki a kasashen nahiyar Afirka.

Ren wanda ya bayyana hakan, yayin ganawar sa da jaridar Ahram ta kasar Masar, ya ce Huawei na da ikon samar da moriya ga kasashen nahiyar, ta hanyar samar da fasahohin sanarwa na zamani. Don haka a cewar sa, kamata ya yi kasashen nahiyar su maida hankali ga tsara manufofin fasahar sadarwa a mataki na kasashen su.

Babban jami'in kamfanin na Huawei ya ce kamata ya yi kasashen Afirka, su maida hankali ga samar da manyan kayayyakin bunkasa fasahar sadarwa, tare da horas da matasan nahiyar dabarun amfani da na'urorin zamani, da fasahar sadarwa, domin tabbatar da cin moriya daga alfanun dake tattare da wannan muhimmin fanni. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China