Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsokanar da aka yi tsakanin Sin da kasashen Afrika matakan banza ne
2019-08-21 10:37:43        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a jiya Talata cewa, shafa kashin kaji kan kasar Sin da duk tsokanar da ake yi wa Sin da kasashen Afrika, matakai marasa amfani da ba zai cimma nasara ba.

A gun taron manema labarai da aka yi a wannan rana, an gabatar da tambayar cewa, jaridar "The Wall Street Journal" ta kasar Amurka ta ba da labarin cewa, kamfanin Huawei na amfani da fasaha da kayayyakinsa, don taimakawa gwamnatocin wasu kasashen Afrika wajen sa ido kan abokan gabansu a cikin kasashen, ciki hadda Uganda da Zambiya. Shin ko mene ne martanin kasar Sin kan wannan batu?

Game da hakan, Geng Shuang ya ce, kamfanin Huawei ya riga ya ba da amsa, kuma gwamnatocin wadannan kasashe ciki hadda Uganda da Zambiya, su ma sun bayyana matsayinsu. Kakakin shugaban Uganda ya ce, jaridar ta ba da wannan labari ba tare da hujja ko dalili ba, kuma ba ta fadi gaskiya ba. Shi kuma takwaransa na Zambiya cewa ya yi, labarin babu adalci ko gaskiya a cikinsa, kuma kasar ba ta amince da labarin ba.

Geng Shuang ya kara da cewa, bisa bukatun wasu kasashen Afrika, Sin ta kara hadin kai da su ta fuskar harkokin 'yan sanda, da tsaro da dai sauransu, don taimaka musu wajen kafa tsarin gudanar da iri wadannan harkoki, ta yin amfani da kimiya da fasaha na zamani, ta yadda za a kyautata halin da al'umominsu ke ciki, na samun kwanciyar hankali da yin ciniki. Matakin da ya samu karbuwa sosai a wurin.

Ya ce yin amfani da kimiyya da fasaha don daga matsayin kyautata zaman rayuwar jama'a, kullum kasashen duniya na yin hakan. Amurka ta amince da amfani da irin wadannan fasaha da kayayyaki a gida, to amma don me sauran kasashe ba za su iya yin hakan ba? Kuma har wasu ke zargin cewa hakan wani mataki ne na sa ido?

Geng Shuang ya kara da cewa, jaridar ta dauki wasu kalmomi don bayyana wani nufi na daban, ba ta da cikakken shaidu, kuma ta kasa fayyace fari da baki. A matsayin wata kafar yada labarai mai shahara a duk duniya, labarin da Jaridar "The Wall Street Journal" ta bayar ya ci mutuncinta kwarai da gaske.

Ya kara da cewa, kasashen Afrika na sane da bukatunsu matuka, kuma suna mai da hankali sosai kan muradu da tsaronsu, kana babu ruwan sauran kasashe da harkokin cikin gidansu. Kaza lika shafawa kasar Sin kashin kaji da duk wata tsokana da za a yiwa Sin da kasashen Afrika, matakan banza ne da ba za su cimma nasara ba. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China