Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ko aka kara tsoma baki a harkokin Hong Kong, amma kasar Sin ba za ta sauya niyyarta ta kafa dokar tsaron kasa a Hong Kong ba
2020-06-12 21:11:50        cri

Dangane da sabon rahoton rabin shekara da gwamnatin kasar Birtaniya ta gabatar kan batun Hong Kong, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Jumma'a a nan Beijing cewa, kasar Sin tana adawa da yadda Birtaniya take tsoma baki a harkokin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Ko da yake wasu kasashe na ci gaba da kara tsoma baki a harkokin Hong Kong, hakika dai kasar Sin ba za ta sauya niyyarta ta kafa dokar tsaron kasa a Hong Kong ko kadan ba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China