Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin kwamishinan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi Allah wadai da kalaman 'yan majalisar dokokin Amurka kan yankin Hong Kong
2019-09-02 10:13:47        cri

Ofishin kwamishinan ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin dake yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin (HKSAR) ya yi Allah wadai da kakkausar murya da kalaman da wasu 'yan majalisun dokokin kasar Amurka suka yi kan yankin na Hong Kong da ma yadda suke tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin.

Wata sanarwa da kakakin ofishin ya fitar a jiya Lahadi, ya kuma yi Allah wadai da yadda 'yan majalisun dokokin Amurka ke tsoma baki a harkokin yankin na Hong Kong, wanda wani bangare na kasar Sin da ba za iya raba shi ba, inda suka danne gaskiya tare da mayar da fari baki bisa mummunar niyyarsu.

Sanarwar mayar da martani ne ga kalaman baya-bayan da shugaban kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin Amurka Eliot Engel da dan majalisa Micheal McCaul suka yi game da abubuwan da tsageru masu tayar bore suka aikata a Hong Kong, wadanda suka keta manufofin gwamnatin tsakiya kan yankin na Hong Kong, tare da nuna yatsa kan dokokin tafiyar da gwamnatin yankin musamman na Hong Kong.

Sama da watanni biyu ke nan ana gudanar da bore a yankin na Hong Kong, lamarin da ya haddasa mummunar illa ga tattalin arziki da yanayin rayuwar jama'a da ma yankin baki daya. Amma duk da haka, a cewar kakakin, wasu 'yan siyasar Amurka na goyon bayan wadannan tsaregu masu tayar da boren na ganin an wargaza yankin Hong Kong.

Kakakin ya ce, kowa ya san cewa, su ne suka haddasa tashin hankalin dake faruwa a yankin Hong Kong, amma burinsu ba zai cika ba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China