Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sassa daban daban na Hong Kong sun goyi bayan matakan mahukuntan yankin na warware matsala
2019-09-17 10:30:26        cri

Jiya ne Kungiyar Sinawa masu shigo da fitar da kayayyaki dake Hong Kong wato HKCIEA ta shirya liyafar murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, kantomar yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ta ce, Hong Kong zai yi amfani da kyakkyawar damar da yake da shi wajen shiga ayyukan raya kasar ta Sin. Kana zai fito da wasu matakan daidaita matsalolin da ake fuskanta yanzu. Sassa daban daban na yankin sun nuna goyon bayansu ga mahukuntan yankin, sun kuma yi imani cewa, yankin Hong Kong zai samu kyakkyawar makoma karkashin manufar nan ta "kasa daya amma tsarin mulkin biyu".

A wannan rana, mista Leung Chun-ying, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, da madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor, da jami'an wasu ofisohin gwamnatin tsakiyar kasar da ke Hong Kong, da jami'an mahukuntan yankin da wakilan 'yan kasuwan yankin sun halarci liyafar. A jawabin da ta gabatar, madam Carrie Lam Cheng Yuet-ngor ta ce, bana, shekara shekaru 70 ke nan da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. Sakamakon yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje cikin shekaru fiye da 40, ya sa kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannonin tattalin arziki, ingantuwar rayuwar jama'a. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China