Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan HK sun tsare mutane 88 biyo bayan zanga-zangar da aka yi ranar Lahadi
2019-11-11 14:20:54        cri

Cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar da safiyar yau Litinin, rundunar 'yan sandan HK ta ce ta tsare mutane 88 bisa laifukan dake da alaka da fasa kantuna da manyan rukunin kantuna da sauran kayayyakin amfanin al'umma.

A cewar rundunar, ya zuwa karfe 11:30 na daren ranar Lahadi, an tsare jimilar mutane 88 saboda laifukan gudanar da zanga-zanga ba bisa ka'ida ba da mallakar makamai da kuma rufe fuskokinsu yayin da suke zanga-zangar da ta sabawa doka.

Sanarwar ta ce 'yan sanda za su ci gaba da matse kaimi wajen kiyaye tsaron al'umma da hukunta masu keta doka.

Gwamnatin yankin da rundunar 'yan sandan, sun yi tir da ayyukan masu zanga-zangar, sannan sun lashi takobin kin lamuntar lalata kayayyakin al'umma. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China