Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a tsaya kan matsayin adalci kan halin da ake ciki a Hong Kong
2019-08-21 15:38:17        cri

A yayin da suke halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin, Japan da Korea ta Kudu karo na 9, ministar harkokin wajen Korea ta Kudu madam Kyung-wha Kang da ministan harkokin wajen Japan Taro Kono sun tambayi ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi halin da ake ciki a yankin musamman na Hong Kong, tare da nuna dan damuwa kan tsaron kamfanoninsu a Hong Kong da kuma tsaron lafiyar mutanensu dake zaune a yankin.

Wang Yi ya jaddada cewa, harkokin Hong Kong, harkokin cikin gida ne na kasar Sin, bai kamata kasashen ketare su tsoma baki ciki ba, kuma kasar Sin ta fahimci damuwar kasashen 2. An yi imani da cewa, mahukuntan Hong Kong za su kiyaye halaltattun hakkokinsu bisa doka. Kana kuma kamata ya yi a fahimta tare da goyon bayan yadda mahukuntan Hong Kong suke kokarin kwantar da kura a yankin bisa doka, a kuma tsaya kan ra'ayi mai adalci. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China