Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zhao Lijian: Bai dace Amurka ta bukaci kwamitin tsaron MDD ya gudanar da zama game da dokar tsaron kasar Sin mai nasaba da Hong Kong ba
2020-05-29 20:56:06        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce bai dace Amurka ta bukaci kwamitin tsaron MDD, ya gudanar da zama game da dokar tsaron kasar Sin mai nasaba da yankin Hong Kong ba. Jami'in na Sin ya ce dalilan da Amurka ta gabatar ba su da ma'ana, kuma yunkurin na ta ba zai yi nasara ba.

Rahotanni sun nuna cewa, Amurka na kallon dokar tsaron kasar Sin a matsayin barazana ga babban 'yancin cin gashin kan Hong Kong, kuma hakan na da alaka da zaman lafiya da lumana na kasa da kasa. A don hakan ne kuma, ta bukaci kwamitin tsaron da ya gudanar da taro ta kafar bidiyo game da wannan batu.

Da yake amsa tambayoyi yayin taron 'yan jaridu da aka saba gudanarwa, Zhao Lijian ya jaddada cewa, ikon kasar Sin ne ta kafa, tare da inganta tsarin dokoki, da hanyoyin aiwatar da su a yankin musamman na Hong Kong, da nufin tabbatar da tsaron kasa a matakin koli, kuma ba wata kasa ta waje da ke da hurumin tsoma baki cikin wannan batu.

Jami'in ya kara da cewa, kwamitin tsaron MDD, ba makami ne da Amurka ke da ikon sarrafawa a duk lokacin da ta so ba. Sin da sauran kasashen duniya masu rajin tabbatar da adalci, ba za su bari Amurka ta yi garkuwa da kwamitin tsaro, domin cimma muradun ta na siyasa ba.

A wani ci gaban kuma, a ranar Alhamis, cikin wata sanarwar hadin gwiwa, Amurka da Birtaniya, da Australia da Canada, sun sanar da cewa, yadda majalissar wakilan jama'ar kasar Sin ta zartas da dokar tsaron kasar Sin mai nasaba da yankin Hong Kong, ta keta hurumin ka'idojin kasa da kasa masu nasaba da yarjejeniyar da Sin da Birtaniya suka cimma, da ma salon mulkin Sin na "kasa daya amma tsarin mulki biyu" da ake aiwatarwa a Hong Kong yanzu.

Game da wannan zargi, Zhao Lijian ya ce Sin na fatan kasashen da wannan batu ya shafa, za su martaba ikon mulkin kai na kasar Sin, su kiyaye kalaman su, da matakai da suke dauka, kana su dakatar da tsoma baki cikin harkokin yankin Hong Kong, da ma sauran harkokin cikin gidan kasar Sin a dukkanin fannoni. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China