Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Nijeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar
2020-06-09 11:13:24        cri

Jakadan kasar Sin dake kasar Nijeriya Zhou Pingjian ya gana da ministan harkokin wajen kasar, Geoffrey Onyeama.

A yayin ganawar tasu, Zhou Pingjian ya yi bayani kan dokar kare tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong, da kuma matsayin kasar Sin kan wannan batu. Ya ce, kudurin da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta yanke ya dace da halin da ake ciki, kuma batun ya kasance harkar cikin gida ta kasar Sin, don haka, bai kamata kasashen ketare su tsoma baki ciki ba, ya ce kasar Sin tana dukufa wajen karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da 'yan uwanta kasashen Afirka, da ma gamayyar kasa da kasa domin yaki da cutar numfashi ta COVID-19, kuma tana fatan kasar Nijeriya za ta iya kare tsaro da lafiyar al'ummomin kasar Sin dake kasar yadda ya kamata.

A nasa bangare kuma, Geoffrey Onyeama ya ce, kasarsa tana goyon bayan manufar kasar Sin daya kacal a duniya, yankin Hong Kong wani bangare ne na kasar Sin, dokar tsaron kasa dake shafar yankin Hong Kong, harka ce ta cikin gidan kasar Sin, kuma Nijeriya tana girmama 'yancin kan kasar Sin sosai. Ya kara da cewa, yaduwar cutar numfashi ta COVID-19 ta zama babban kalubale ga kasa da kasa, inda ya ce Nijeriya na son yin mu'amala da hadin gwiwa da kasar Sin wajen yaki da cutar, kuma za ta dukufa wajen kiyaye tsaro da lafiyar al'ummar Sin dake Nijeriya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China